Littafi Mai Tsarki

Zab 86:9-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Dukan sauran al'umma da ka halittaZa su zo su rusuna har ƙasa a gabanka.Za su yabi girmanka,

10. Gama kai kaɗai ne Maɗaukaki, ya Allah,Kai kaɗai ne ka aikata abubuwa na banmamaki.

11. Ya Ubangiji, ka koya mini abin da kake so in yi,Ni kuwa zan yi maka biyayya da aminci.Ka koya mini in bauta maka da zuciya ɗaya.

12. Zan yabe ka da zuciya ɗaya, ya Ubangiji Allahna,Zan riƙa shelar girmanka har abada.

13. Wane irin girma madawwamiyar ƙaunarka take da shi a gare ni!Gama ka cece ni daga zurfin kabari.

14. Masu girmankai sun tasar mini, ya Allah,Ƙungiyar mugaye tana ƙoƙari ta kashe ni,Mutanen da ba su kula da kai ba.

15. Ya Ubangiji, kai Allah ne mai jinƙai, mai ƙauna,Mai jinkirin fushi, kullum kai mai alheri ne, mai aminci.

16. Ka juyo gare ni, ka yi mini jinƙai,Ka ƙarfafa ni, ka cece ni,Gama ina bauta maka, kamar yadda mahaifiyata ta yi.

17. Ka nuna mini alherinka, ya Ubangiji,Sa'an nan su waɗanda suke ƙina za su sha kunya,Sa'ad da suka ga ka ta'azantar da ni,Ka kuma taimake ni.