Littafi Mai Tsarki

Zab 69:4-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Waɗanda suke ƙina ba daliliSun fi gashin kaina yawa,Waɗanda suke baza ƙarya suke ƙina,Suna da ƙarfi, suna kuwa so su kashe ni.Suka tilasta ni in mayar da abubuwan da ba satarsu na yi ba.

5. Zunubaina ba a ɓoye suke a gare ka ba ya Allah,Ka san irin wawancin da na yi!

6. Kada ka bar ni in jawo kunya ga waɗanda suka dogara gare ka,Ya Ubangiji Allah Mai Iko Dukka!Kada ka bar ni in jawo abin kunyaGa waɗanda suke maka sujada, ya Allah na Isra'ila!

7. Sabili da kai ne aka ci mutuncina,Kunya ta rufe ni.

8. Kamar baƙo nake ga 'yan'uwana,Haka ma ga iyalina, kamar baƙo nake.

9. Ƙaunar da nake da ita ta yin ibada a HaikalinkaTana iza ni a ciki kamar wuta,Zargin da suke yi a kanka, ya fāɗa a kaina.

10. Na ƙasƙantar da kaina ta wurin yin azumi,Jama'a kuwa suka ci mutuncina.

11. Na sa tufafin makoki,Sai suka maishe ni abin dariya.

12. A tituna suna ta magana a kaina,Bugaggu da giya kuwa suna raira waƙa a kaina.

13. Amma ni, zan yi addu'a gare ka, ya Ubangiji,Ka amsa mini, ya Allah, a lokacin da ka zaɓa,Sabili da muhimmiyar ƙaunarka,Saboda kana cika alkawarinka na yin ceto.

14. Ka cece ni daga nutsewa cikin wannan laka,Ka kiyaye ni daga maƙiyana,Daga kuma wannan ruwa mai zurfi.

15. Kada ka bar ambaliyar ruwa ta rufe ni.Kada ka bar ni in mutu cikin zurfafa,Ko in nutse a cikin kabari.

16. Sabili da madawwamiyar ƙaunarka, ka amsa mini, ya Ubangiji,Ka juyo wurina, saboda juyayinka mai girma!

17. Kada ka ɓoye kanka daga bawanka,Ina shan babbar wahala, ka yi hanzari ka amsa mini!

18. Ka zo ka fanshe ni,Ka kuɓutar da ni daga abokan gābana.

19. Ka san yadda ake cin mutuncina,Da yadda ake kunyata ni, ake ƙasƙantar da ni,Kana ganin dukan abokan gābana.