Littafi Mai Tsarki

Zab 64:4-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Sukan yi kwanto su harbi mutanen kirki da kibau,Nan da nan sukan yi harbi, ba su kuwa jin tsoro.

5. Suna ƙarfafa junansu cikin yin mugayen ƙulle-ƙullensu,Sukan yi ta taɗi a kan inda za su kafa tarkunansu.“Ba wanda zai gan mu,” in ji su.

6. Sukan shirya maƙarƙashiya, su ce,“Ai, mun gama shirin aikata laifi sarai.”Zuciyar mutum da tunaninsa, suna da wuyar ganewa!

7. Amma Allah zai harbe su da kibansa,Za a yi musu rauni nan da nan.

8. Zai hallaka su saboda maganganunsu,Duk wanda ya gan su zai kaɗa kansa.

9. Dukansu za su ji tsoro,Za su faɗi abin da Allah ya aikata,Su yi tunani a kan ayyukansa.

10. Dukan masu adalci za su yi murna,Saboda abin da Ubangiji ya aikata.Za su sami mafaka a gare shi,Dukan mutanen kirki za su yabe shi.