Littafi Mai Tsarki

Zab 64:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ina shan wahala, ya Allah, ka ji addu'ata!Ina jin tsoro, ka cece ni daga maƙiyana!

2. Ka kiyaye ni daga ƙulle-ƙullen mugaye,Da iskancin mugayen mutane.

3. Sukan wasa harsunansu kamar takuba,Sukan kai bāra da mugayen maganganu kamar kibau.

4. Sukan yi kwanto su harbi mutanen kirki da kibau,Nan da nan sukan yi harbi, ba su kuwa jin tsoro.

5. Suna ƙarfafa junansu cikin yin mugayen ƙulle-ƙullensu,Sukan yi ta taɗi a kan inda za su kafa tarkunansu.“Ba wanda zai gan mu,” in ji su.

6. Sukan shirya maƙarƙashiya, su ce,“Ai, mun gama shirin aikata laifi sarai.”Zuciyar mutum da tunaninsa, suna da wuyar ganewa!

7. Amma Allah zai harbe su da kibansa,Za a yi musu rauni nan da nan.

8. Zai hallaka su saboda maganganunsu,Duk wanda ya gan su zai kaɗa kansa.