21. Kalmominsa sun fi mai taushi,Amma ƙiyayya tana a zuciyarsa,Kalmominsa sun fi mai sulɓi,Amma suna yanka kamar kakkaifan takobi.
22. Ka gabatar da wahalarka ga Ubangiji,Zai kuwa taimake ka,Ba zai bari a ci nasara a kan mutumin kirki ba, faufau.
23. Amma kai, ya Allah, za ka jefar da masu kisankai, da maƙaryata can ƙasa cikin zurfafa,Kafin su kai rabin kwanakinsu a duniya.Amma ni, zan dogara gare ka.