Littafi Mai Tsarki

Yahu 1:14-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Anuhu ma wanda yake na bakwai daga Adamu, shi ma ya yi annabci a kan waɗannan mutane cewa, “Ga shi, Ubangiji ya zo da dubban tsarkakansa,

15. don ya zartar da hukunci kan kowa, yă kuma tabbatar wa marasa bin Allah dukan aikinsu na rashin bin Allah, da suka aikata ta hanyar rashin bin Allah, da kuma baƙaƙen maganganu da masu zunubi marasa bin Allah suka yi game da shi.”

16. Waɗannan su ne masu gunaguni, masu ƙunƙuni, masu biye wa muguwar sha'awa, marubata, masu yi wa mutane bambaɗanci don samun wata fa'ida.

17. Ya ku ƙaunatattuna, lalle ku tuna da maganar da manzannin Ubangijinmu Yesu Almasihu suka faɗa a dā,

18. da suka ce da ku, “A zamanin ƙarshe za a yi waɗansu mutane masu ba'a, masu biye wa muguwar sha'awarsu ta rashin bin Allah.”

19. Waɗannan su ne masu raba tsakani, masu son zuciya, marasa Ruhu.

20. Amma ya ku ƙaunatattuna, ku riƙa inganta kanku ga bangaskiyarku mafi tsarki, kuna addu'a da ikon Ruhu Mai Tsarki.