Littafi Mai Tsarki

Mar 6:17-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Don dā Hirudus da kansa ya aika aka kamo Yahaya, ya ɗaure shi a kurkuku saboda Hirudiya matar ɗan'uwansa Filibus, wadda shi Hirudus ya aura.

18. Don dā Yahaya ya ce wa Hirudus, “Bai halatta ka zauna da matar ɗan'uwanka ba.”

19. Hirudiya kuwa na riƙe da Yahaya cikin zuciyarta, har ta so ta kashe shi, amma ba ta sami hanya ba,

20. don Hirudus yana tsoron Yahaya, ya sani shi mutum ne adali, tsattsarka, shi ya sa ya kāre shi. Hirudus yakan damu da yawa sa'ad da yake sauraron Yahaya, ko da yake na murna da jinsa.

21. Amma wani sanadi ya zo, da ranar haihuwar Hirudus ta kewayo, ya yi wa hakimansa, da sarakunan yaƙinsa, da kuma manyan ƙasar Galili biki.

22. Da 'yar Hirudiya ta shigo ta yi rawa, sai ta gamshi Hirudus da baƙinsa. Sai fa sarki ya ce wa yarinyar, “Roƙe ni kome, sai in ba ki.”

23. Ya kuma rantse mata, ya ce, “Kome kika roƙe ni zan ba ki, ko da rabin mulkina ne.”

24. Ta fita, ta ce wa uwa tata, “Me zan roƙa?” Uwar ta ce, “Kan Yahaya Maibaftisma.”