Littafi Mai Tsarki

Mar 14:28-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. Amma fa bayan an tashe ni, zan riga ku zuwa ƙasar Galili.”

29. Bitrus ya ce masa, “Ko duk sun yi tuntuɓe, ni kam, ba zan yi ba.”

30. Sai Yesu ya ce masa, “Hakika, ina gaya maka, ko a wannan dare, kafin zakara ya yi cara ta biyu, za ka yi musun sanina sau uku.”

31. Amma Bitrus ya yi ta nanatawa da ƙarfi yana cewa, “Ko da za a kashe ni tare da kai, ba zan yi musun saninka ba.” Dukansu ma haka suka ce.

32. Sai suka isa wani wuri, wai shi Getsamani. Ya ce wa almajiransa, “Ku zauna nan har in yi addu'a.”

33. Sai ya ɗauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, ya kuma fara jin wahala gaya, yana damuwa ƙwarai.

34. Sai ya ce musu, “Raina na shan wahala matuƙa, har ma kamar na mutu. Ku dakata nan, ku zauna a faɗake.”

35. Da ya ci gaba kaɗan, sai ya faɗi ƙasa, ya yi addu'a ko ya yiwu a ɗauke masa wannan lokaci.