Littafi Mai Tsarki

Mar 11:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da suka kusato Urushalima, da Betafaji, da Betanya, wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa biyu,

2. ya ce musu, “Ku shiga ƙauyen can da yake gabanku. Da shigarku za ku ga wani aholaki a ɗaure, wanda ba a taɓa hawa ba. Ku kwanto shi.

3. Kowa ya ce muku, ‘Don me kuke haka?’ ku ce, ‘Ubangiji ne yake bukatarsa, Zai kuma komo da shi nan da nan.’ ”

4. Sai suka tafi, suka tarar da aholakin a ɗaure a ƙofar gida a bakin hanya, suka kwance shi.

5. Sai waɗanda suke tsaitsaye a gun suka ce musu, “Don me kuke kwance aholakin nan?”

6. Suka faɗa musu abin da Yesu ya ce. Su kuwa suka ƙyale su suka tafi.

7. Suka kawo wa Yesu aholakin, suka shimfiɗa mayafansu a kai, ya hau.

8. Sai mutane da yawa suka shisshimfiɗa mayafansu a hanya, waɗansu kuma suka baza ganyen da suka kakkaryo a saura.

9. Da na gaba da na baya suka riƙa sowa suna cewa, “Hosanna! Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji!

10. Albarka ta tabbata ga mulkin nan mai zuwa na ubanmu Dawuda! Hosanna ga Allah!”