Littafi Mai Tsarki

Mar 10:46-52 Littafi Mai Tsarki (HAU)

46. Sai suka iso Yariko. Yana fita daga Yariko ke nan, da shi, da almajiransa, da wani ƙasaitaccen taro, sai ga wani makaho mai bara, wai shi Bartimawas, ɗan Timawas, yana zaune a gefen hanya.

47. Da ya ji dai Yesu Banazare ne, sai ya fara ɗaga murya yana cewa, “Ya Yesu, Ɗan Dawuda, ka ji tausayina!”

48. Waɗansu da yawa suka kwaɓe shi, cewa ya yi shiru. Amma sai ƙara ɗaga murya yake yi ƙwarai da gaske, yana cewa, “Ya Ɗan Dawuda, ka ji tausayina!”

49. Sai Yesu ya tsaya ya ce, “Ku kirawo shi.” Sai suka kirawo makahon suka ce masa, “Albishirinka! Taso, yana kiranka.”

50. Sai ya yar da mayafinsa, ya zaburo wurin Yesu.

51. Yesu ya ce masa, “Me kake so in yi maka?” Makahon ya ce masa, “Malam, in sami gani!”

52. Sai Yesu ya ce masa, “Yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai.” Nan take ya gani, ya bi Yesu, suka tafi.