Littafi Mai Tsarki

M. Had 2:11-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Na yi tunani a kan dukan abin da na aikata, da irin wahalar da na sha lokacin da nake yin aikin, sai na gane ba shi da wata ma'ana, na zama kamar mai harbin iska, ba shi da wani amfani.

12. Bayan wannan duka, abin da sarki zai iya yi kaÉ—ai, shi ne abin da sarakunan da suka riga shi suka yi.Sai na fara tunani a kan abin da ake nufi da hikima, ko rashin kula, ko wauta.

13. To, na sani hikima ta fi wauta, kamar yadda haske ya fi duhu.

14. Mai hikima ya san inda ya nufa, amma wawa ba zai iya sani ba. Na kuma sani makomarsu guda ce.