Littafi Mai Tsarki

M. Had 11:8-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Idan mutum ya rayu har shekaru da yawa, bari ya yi murna a cikinsu duka. Sai dai kuma ya tuna da kwanakin duhu, gama sun fi yawa. Duk abin da ya faru banza ne.

9. Ya saurayi! Ka yi murna a lokacin ƙuruciyarka, ka bar zuciyarka ta yi farin ciki a kwanakin samartakarka. Ka bi nufin zuciyarka da sha'awar idanunka. Amma ka sani fa, a cikin al'amuran nan duka Allah zai shara'anta ka.

10. Kada ka bar kome ya dame ka, ko ya yi maka zafi a rai, gama ƙuruciya da samartaka ba za su dawwama ba.