Littafi Mai Tsarki

Luk 9:44-60 Littafi Mai Tsarki (HAU)

44. “Maganar nan fa tă shiga kunnenku! Za a ba da Ɗan Mutum ga mutane.”

45. Amma ba su fahimci maganan nan ba, an kuwa ɓoye musu ita ne don kada su gane. Su kuwa suna tsoron tambayarsa wannan magana.

46. Sai musu ya tashi a tsakaninsu a kan ko wane ne babbansu.

47. Amma da Yesu ya gane tunanin zuciyarsu, ya kama hannun wani ƙaramin yaro ya ajiye shi kusa da shi.

48. Ya ce musu, “Duk wanda ya karɓi ƙanƙane yaro kamar wannan saboda sunana, ni ya karɓa. Wanda kuwa ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ke nan. Ai, wanda yake ƙarami a cikinku shi ne babba.”

49. Sai Yahaya ya amsa ya ce, “Maigida, mun ga wani yana fitar da aljannu da sunanka, mun kuwa hana shi, domin ba ya binmu.”

50. Amma Yesu ya ce masa, “Kada ku hana shi. Ai, duk wanda ba ya gāba da ku, naku ne.”

51. Da lokacin karɓarsa a Sama ya gabato, ya himmantu sosai ga zuwa Urushalima.

52. Sai ya aiki jakadu su riga shi gaba, suka kuwa tafi suka shiga wani ƙauyen Samariyawa su shisshirya masa.

53. Amma Samariyawa suka ƙi karɓarsa, domin niyyarsa duk a kan Urushalima take.

54. Da almajiransa Yakubu da Yahaya suka ga haka suka ce, “Ya Ubangiji, ko kana so mu umarci wuta ta sauko daga sama ta lashe su?”

55. Amma ya juya, ya tsawata musu.

56. Sai suka ci gaba, suka tafi wani ƙauye.

57. Suna tafiya a hanya, sai wani mutum ya ce masa, “Zan bi ka duk inda za ka.”

58. Yesu ya ce masa, “Yanyawa da ramummukansu, tsuntsaye kuma da wurin kwanansu, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin shaƙatawa.”

59. Ya kuma ce wa wani, “Bi ni.” Sai ya ce, “Ya Ubangiji, ka bar ni tukuna in je in binne tsohona.”

60. Sai Yesu ya ce masa, “Bari matattu su binne 'yan'uwansu matattu. Amma kai kuwa, tafi ka sanar da Mulkin Allah.”