Littafi Mai Tsarki

Luk 6:38-43 Littafi Mai Tsarki (HAU)

38. Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har ya yi tozo, har yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna, da shi za a auna muku.”

39. Ya kuma ba su wani misali ya ce, “Makaho yana iya yi wa makaho jagora? Ashe, dukansu biyu ba sai su fāɗa a rami ba?

40. Almajiri ba ya fin malaminsa. Amma kowa aka karantar da shi sosai, sai ya zama kamar malaminsa.

41. Don me kake duban ɗan hakin da yake a idon ɗan'uwanka, amma gungumen da yake a naka ido ba ka kula ba?

42. Ƙaƙa kuma za ka iya ce wa ɗan'uwanka, ‘Ya ɗan'uwana, bari in cire maka ɗan hakin da yake a idonka,’ alhali kuwa kai kanka ba ka ga gungumen da yake a naka ido ba? Kai munafuki! Sai ka fara cire gungumen da yake a idonka tukuna sa'an nan ka gani sosai yadda za ka cire ɗan hakin da yake a idon ɗan'uwanka.”

43. “Ba kyakkyawan itace da yake haifar munanan 'ya'ya, ba kuma mummunan itace da yake haifar kyawawan 'ya'ya.