Littafi Mai Tsarki

Luk 22:60-71 Littafi Mai Tsarki (HAU)

60. Amma Bitrus ya ce, “Haba, ban ma san abin da kake faɗa ba.” Nan take, kafin ya rufe baki, sai zakara ya yi cara.

61. Sai Ubangiji ya juya ya dubi Bitrus. Bitrus kuwa ya tuna da maganar da Ubangiji ya faɗa masa cewa, “A yau ma kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku.”

62. Sai ya fita waje, ya yi ta rusa kuka.

63. Sai mutanen da suke riƙe da Yesu suka yi ta masa ba'a, suna dūkansa.

64. Suka ɗaure masa idanu, suka tambaye shi, suka ce, “Yi annabci! Wa ya buge ka?”

65. Suka kuma yi ta masa baƙaƙen maganganu masu yawa, suna zaginsa.

66. Da gari ya waye sai majalisar shugabannin jama'a ta haɗu, da manyan firistoci da kuma malaman Attaura. Suka kai shi ɗakin majalisarsu suka ce,

67. “To, in kai ne Almasihu, gaya mana.” Amma ya ce musu, “Ko na gaya muku, ba za ku gaskata ba.

68. In kuma na yi muku tambaya, ba za ku mai da jawabi ba.

69. Amma nan gaba, Ɗan Mutum zai zauna dama na Allah Mai iko.”

70. Duk suka ce, “Ashe, kai ɗin nan Ɗan Allah ne?” Sai ya ce musu, “Yadda kuka faɗa, ni ne.”

71. Sai suka ce, “Wace shaida kuma za mu nema? Ai, mun ji da kanmu daga bakinsa.”