Littafi Mai Tsarki

Luk 22:13-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Sai suka tafi, suka kuwa tarar kamar yadda ya faɗa musu, suka shirya Jibin Ƙetarewa.

14. Da lokaci ya yi, sai ya zauna cin abinci, manzanninsa kuma suna tare da shi.

15. Ya ce musu, “Ina so ƙwarai ko dā ma in ci jibin nan na Ƙetarewa tare da ku, kafin in sha wuya.

16. Gama ina gaya muku ba zan ƙara cin sa ba, sai an cika shi a Mulkin Allah.”

17. Sai ya karɓi ƙoƙo, bayan da ya yi godiya ga Allah, ya ce, “Ungo wannan, ku shassha.

18. Ina gaya muku, daga yanzu, ba zan ƙara shan ruwan inabi ba, sai Mulkin Allah ya bayyana.”

19. Sai ya ɗauki gurasa, bayan da ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba su, ya ce, “Wannan jikina ne da za a bayar dominku. Ku riƙa yin haka, domin tunawa da ni.”

20. Haka kuma, bayan jibi, ya ɗauki ƙoƙon, ya ce, “Ƙoƙon nan sabon alkawari ne, da aka tabbatar da jinina da za a bayar dominku.

21. Amma ga shi, mai bashe ni ɗin nan yana ci a akushi ɗaya da ni.

22. Lalle Ɗan Mutum zai ƙaura kamar yadda aka ƙaddara, duk da haka, kaiton mutumin nan da yake ba da shi!”

23. Sai suka fara tambayar juna ko wane ne a cikinsu zai yi haka.

24. Sai musu ya tashi a tsakaninsu, a kan ko wane ne babbansu.

25. Sai ya ce musu, “Sarakunan al'ummai sukan nuna musu iko, mahukuntansu kuma sukan nema a ce da su, ‘Mataimakan jama'a.’

26. Amma ku kam ba haka ba. Sai dai wanda yake babba a cikinku yă zama kamar ƙarami, shugaba kuwa yă zama kamar mai hidima.

27. Wa ya fi girma? Wanda ya zauna cin abinci, ko kuwa mai hidimar? Ashe, ba wanda ya zauna cin abinci ba ne? Ga shi kuwa, ina a cikinku kamar mai hidima.

28. “Ku ne kuka tsaya gare ni a gwaje-gwajen da na sha.