Littafi Mai Tsarki

Luk 20:36-47 Littafi Mai Tsarki (HAU)

36. Ba shi yiwuwa su sāke mutuwa, don daidai suke da mala'iku, 'ya'yan Allah ne kuwa, da yake 'ya'yan tashin matattu ne.

37. Game da tashin matattu kuwa, ai, Musa ma ya faɗa, a labarin kurmin, inda ya kira Ubangiji, Allahn Ibrahim, da Allahn Ishaku, da Allahn Yakubu.

38. Ai, waɗanda Allah shi ne Allahnsu rayayyu ne, ba matattu ba. Don a wurinsa duka rayayyu ne.”

39. Sai waɗansu malaman Attaura suka amsa suka ce, “Malam, ka faɗi daidai.”

40. Daga nan kuma ba su yi ƙarfin halin tambayarsa wani abu ba.

41. Amma ya ce musu, “Ƙaƙa za su ce Almasihu ɗan Dawuda ne?

42. Domin Dawuda da kansa a Zabura ya ce,‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,“Zauna a damana,

43. Sai na sa ka take maƙiyanka.” ’

44. Dawuda ya ce shi Ubangiji ne. To, ƙaƙa zai zama ɗansa?”

45. Ya ce wa almajiransa a gaban dukan jama'a,

46. “Ku yi hankali da malaman Attaura, masu son yawo a cikin manyan riguna, masu so a gaishe su a kasuwa, masu son mafifitan mazaunai a majami'u, da mazaunan alfarma a wurin biki.

47. Su ne masu cin kayan matan da mazansu suka mutu, masu yin doguwar addu'a don ɓad da sawu. Su za a yi wa hukunci mafi tsanani.”