Littafi Mai Tsarki

Luk 2:27-46 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. Ruhu na iza shi, sai ya shiga Haikalin. Da iyayen suka shigo da ɗan yaron nan Yesu, su yi masa yadda ka'idar Shari'ar ta ce,

28. sai Saminu ya rungume shi, ya yi wa Allah godiya, ya ce,

29. “Yanzu kam, ya Mamallaki,Sai ka sallami bawanka lafiya,Bisa ga abin da ka faɗa,

30. Don na ga cetonka zahiri,

31. Da ka shirya a gaban kabilai duka,

32. Haske mai bayyana wa alummai hanyarka,Da kuma ɗaukakar jama'arka Isra'ila.”

33. Uwa tasa da ubansa kuwa suna mamakin abin da aka faɗa game da shi,

34. Sai Saminu ya sa musu albarka, ya ce wa Maryamu uwar Yesu,“Kin ga wannan yaro, shi aka sa ya zama sanadin faɗuwar waɗansu, tashin waɗansu kuma da yawa cikin Isra'ila,Zai kuma zama alama wadda ake kushenta,

35. Domin tunanin zukata da yawa su bayyana.I, ke ma, takobi zai tsaga zuciyarki.”

36. Akwai kuma wata annabiya, mai suna Hannatu, 'yar Fanuyila, na kabilar Ashiru. Ta kuwa tsufa ƙwarai, ta yi zaman aure shekara bakwai bayan ɗaukanta na budurci,

37. da mijinta ya mutu kuma ta yi zaman gwauranci har shekara tamanin da huɗu. Ba ta rabuwa da Haikalin, tana bauta wa Allah dare da rana ta wurin yin addu'a da azumi.

38. Nan take ita ma ta zo, ta yi wa Allah godiya, ta kuma yi maganar ɗan yaron nan ga dukan masu sauraron fansar Urushalima.

39. Bayan sun ƙare kome da kome bisa ga Shari'ar Ubangiji, sai suka koma ƙasar Galili suka tafi garinsu Nazarat.

40. Ɗan yaron kuwa ya girma, ya kawo ƙarfi, yana mai matuƙar hikima. Alherin Allah kuwa yana tare da shi.

41. To, iyayensa sukan je Urushalima kowace shekara a lokacin Idin Ƙetarewa.

42. Da ya shekara goma sha biyu, sai suka tafi tare da shi bisa ga al'adarsu a lokacin Idi.

43. Da aka gama idin kuma, suna cikin komowa, sai yaron, wato Yesu, ya tsaya a Urushalima, ba da sanin iyayensa ba.

44. Su kuwa suka yi ta tafiya yini guda, suna zaton yana cikin ayari. Sai suka yi ta cigiyarsa cikin 'yan'uwansu da idon sani.

45. Da ba su same shi ba, suka koma Urushalima, suna ta cigiyarsa.

46. Sai kuma a rana uku suka same shi a Haikalin zaune a tsakiyar malamai, yana sauraronsu, yana kuma yi musu tambayoyi.