Littafi Mai Tsarki

Luk 2:20-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Makiyayan suka koma, suna ta ɗaukaka Allah, suna yabonsa, saboda duk abin da suka ji, suka kuma gani, yadda aka gaya musu.

21. Da rana ta takwas ta kewayo da za a yi masa kaciya, aka sa masa suna Yesu, wato sunan da mala'ika ya faɗa kafin ya zauna a ciki.

22. Da kwanakin tsarkakewarsu suka cika bisa ga Shari'ar Musa, suka kawo shi Urushalima, su miƙa shi ga Ubangiji

23. (kamar dai yadda yake a rubuce a Shari'ar Ubangiji cewa, “Duk ɗan farin da aka haifa, za a ce da shi tsattsarka ne Ubangiji”),

24. su kuma yi hadaya bisa ga abin da aka faɗa a Shari'ar Ubangiji cewa, “Kurciyoyi biyu, ko kuwa 'yan shila biyu.”

25. To, akwai wani mutum a Urushalima, mai suna Saminu, adali, mai bautar Allah, yana kuma ɗokin ganin ta'aziyyar Isra'ila. Ruhu Mai Tsarki kuwa yana tare da shi.

26. Ruhu Mai Tsarki kuwa ya riga ya bayyana masa, cewa ba zai mutu ba sai ya ga Almasihun Ubangiji.

27. Ruhu na iza shi, sai ya shiga Haikalin. Da iyayen suka shigo da ɗan yaron nan Yesu, su yi masa yadda ka'idar Shari'ar ta ce,

28. sai Saminu ya rungume shi, ya yi wa Allah godiya, ya ce,