Littafi Mai Tsarki

Luk 17:11-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Wata rana yana tafiya Urushalima, sai ya bi iyakar ƙasar Samariya da Galili.

12. Yana shiga wani ƙauye ke nan, sai waɗansu kutare maza guda goma suka tarye shi, suna tsaye daga nesa.

13. Sai suka ɗaga murya suka ce, “Ya Maigida Yesu, ka ji tausayinmu,”

14. Da ya gan su, ya ce musu, “Ku je wurin firistoci su gan ku.” Suna tafiya ke nan, sai suka tsarkaka.

15. Ɗayansu kuma da ganin an warkar da shi, ya komo, yana ta ɗaukaka Allah da murya mai ƙarfi,

16. ya fāɗi a gaban Yesu, yana gode masa. Shi kuwa Basamariye ne.

17. Yesu ya amsa ya ce, “Ba goma ne aka tsarkake ba? Ina taran?

18. Ashe, ba wanda aka samu ya komo ya ɗaukaka Allah, sai baƙon nan kaɗai?”

19. Sai Yesu ya ce masa, “Tashi, ka yi tafiyarka. Bangaskiyarka ta warkar da kai.”