Littafi Mai Tsarki

Luk 16:26-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. Banda wannan ma duka, tsakaninmu da ku akwai wani gawurtaccen rami mai zurfi, zaunanne, don waɗanda suke son ƙetarewa zuwa wurinku kada su iya, kada kuma kowa ya ƙetaro zuwa wurinmu daga can.’

27. Sai mai arzikin ya ce, ‘To, ina roƙonka, Baba, ka aika shi zuwa gidan ubana,

28. don ina da 'yan'uwa biyar maza, ya je ya yi musu gargaɗi, kada su ma su zo wurin azabar nan.’

29. Amma Ibrahim ya ce, ‘Ai, suna da littattafan Musa da na annabawa, su saurare su mana.’

30. Sai ya ce, ‘A'a, Baba Ibrahim, in dai wani daga cikin matattu ya je wurinsu sa tuba.’

31. Ibrahim ya ce masa, ‘In dai har ba su saurari littattafan Musa da na annabawa ba, ko da wani ya tashi daga cikin matattu ma, ba za su rinjayu ba.’ ”