Littafi Mai Tsarki

Luk 12:18-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Ya kuma ce, ‘To, ga abin da zan yi. Sai in rushe rumbunana, in gina waɗansu manya, in zuba duk amfanin gonata da kayana a ciki.

19. Zan kuma ce wa raina, “Lalle ina da kaya masu yawa a jibge, tanadin shekara da shekaru. Bari in huta, in yi ta ci, in yi ta sha, ina shagali.” ’

20. Amma Allah ya ce masa, ‘Kai marar azanci! A daren nan za a karɓi ranka. To, kayan da ka tanada, na wa za su zama?’

21. Haka, wanda ya tanada wa kansa dukiya yake, ba shi kuwa da wani tanadi a gun Allah.”

22. Sai ya ce wa almajiransa, “Don haka, ina gaya muku, kada ku damu da batun rayuwarku game da abin da za ku ci, ko kuma jikinku, abin da za ku yi sutura.

23. Domin rai ya fi abinci, jiki kuma ya fi tufafi.

24. Ku dubi dai hankaki! Ai, ba sa shuka, ba sa girbi, ba su da taska ko rumbu, amma kuwa Allah yana cishe su. Sau nawa martabarku ta ninka ta tsuntsaye!”

25. Wane ne a cikinku don damuwarsa zai iya ƙara ko da taƙi ga tsawon rayuwarsa?