Littafi Mai Tsarki

Luk 11:39-47 Littafi Mai Tsarki (HAU)

39. Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ku Farisiyawa kam, kukan wanke bayan ƙwarya da akushi, amma a ciki cike kuke da zalunci da mugunta.

40. Ku marasa azanci! Ashe, wanda ya yi bayan, ba shi ya yi cikin ba?

41. Gara ku tsarkake cikin, sa'an nan kome zai tsarkaka a gare ku.

42. “Kaitonku, Farisiyawa! Ga shi, kuna fitar da zakkar na'ana'a da karkashi, da kuma kowane ganyen miya. Amma kun ƙi kula da aikata gaskiya da ƙaunar Allah. Waɗannan ne ya kamata ku yi, ba tare da yar da waɗancan ba.

43. Kaitonku, Farisiyawa! Ga shi, kuna son mafifitan mazaunai a majami'u, da kuma gaisuwa a kasuwa.

44. Kaitonku! Kuna kama da kaburburan da ba a gani, waɗanda mutane suke takawa da rashin sani.”

45. Sai wani a cikin masanan Attaura ya amsa masa ya ce, “Malam, faɗar haka fa, mu ma, ai, ka ci mutuncinmu.”

46. Sai Yesu ya ce, “Ku kuma kaitonku, masanan Attaura! Don kuna jibga wa mutane kaya masu wuyar ɗauka, ku da kanku ko ɗan yatsa ba kwa sawa ku tallafa musu!

47. Kaitonku! Don kuna gina gubbobin annabawan da kakanninku suka kashe.