Littafi Mai Tsarki

Luk 10:37-42 Littafi Mai Tsarki (HAU)

37. Sai ya ce, “Wanda ya nuna masa jinƙai.” Sai Yesu ya ce masa, “Kai ma, ka je ka riƙa yin haka.”

38. Suna tafiya, sai ya shiga wani ƙauye, wata mace kuma mai suna Marta ta sauke da shi a gidanta.

39. Tana kuwa da 'yar'uwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a gaban Ubangiji tana sauraron magana tasa.

40. Marta kuwa yawan hidimomi ya ɗauke mata hankali, sai ta je gunsa, ta ce, “Ya Ubangiji, ba ka kula ba, 'yar'uwata ta bar ni ina hidima ni kaɗai? Gaya mata ta taimake ni mana.”

41. Amma Ubangiji ya amsa mata ya ce, “Marta, Marta! Hankalinki a tashe yake, kina kuma damuwa kan abu da yawa.

42. Bukatu kima ne, ta ainihi ɗaya ce. Maryamu ta zaɓi abu mai kyau, ba kuwa za a karɓe mata ba.”