Littafi Mai Tsarki

Luk 1:76-80 Littafi Mai Tsarki (HAU)

76. Kai kuma, ɗan yarona, za a ce da kai annabin Maɗaukaki,Gama za ka riga Ubangiji gaba,Domin ka shisshirya hanyoyinsa,

77. Kă sanar da ceto ga jama'a tasa,Wato ta samun gafarar zunubansu,

78. Saboda tsananin jinƙai na Allahnmu,Daga Sama hasken asubahi zai ɓullo mana,Daga can Sama ne fa zai keto mana,

79. Domin yă haskaka na zaune cikin duhu,Da waɗanda suke zaune a bakin mutuwa,Domin ya bishe mu a hanyar salama.”

80. Sai ɗan yaron ya girma, ya ƙarfafa a ruhu. Ya kuwa zauna a jeji har ranar bayyanarsa ga Isra'ila.