Littafi Mai Tsarki

L. Mah 3:5-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Saboda haka jama'ar Isra'ila suka zauna tare da Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa.

6. Suka yi aurayya da su, suka kuma yi sujada ga gumakansu.

7. Jama'ar Isra'ila kuwa suka manta da Ubangiji Allahnsu, suka yi masa zunubi, suka yi wa gumakan nan Ba'al da Ashtarot sujada.

8. Domin haka Ubangiji ya husata ƙwarai da Isra'ilawa, sai ya bashe su ga Kushan-rishatayim, Sarkin Mesofotamiya. Jama'ar Isra'ila kuwa suka bauta masa shekara takwas.

9. Amma sa'ad da Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, sai Ubangiji ya ta da Otniyel, ɗan Kenaz, ƙanen Kalibu don ya ceci Isra'ilawa.

10. Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko masa domin ya hukunta Isra'ilawa. Ya fita ya yi yaƙi da Kushan-rishatayim, Sarkin Mesofotamiya. Ubangiji kuwa ya ba da sarkin a hannun Otniyel, ya rinjaye shi.

11. Ƙasar ta sami zaman lafiya shekara arba'in sa'an nan Otniyel, ɗan Kenaz ya rasu.

12. Jama'ar Isra'ila kuma suka sāke yin zunubi a gaban Ubangiji, Ubangiji kuwa ya sa Eglon Sarkin Mowab ya yi ƙarfi, domin ya yi gaba da su.

13. Sai ya tattaro Amoriyawa da Amalekawa, ya je ya ci Isra'ilawa, ya mallaki birnin dabino, wato Yariko.

14. Isra'ilawa suka bauta wa Eglon Sarkin Mowab, shekara goma sha takwas.

15. Amma sa'ad da Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, ya ba su wanda zai cece su, wato Ehud, ɗan Gera daga kabilar Biliyaminu, shi kuwa bahago ne. Isra'ilawa suka aika wa Eglon Sarkin Mowab da kyautai ta hannun Ehud.

16. Sai Ehud ya ƙera wa kansa takobi mai kaifi biyu, tsawonsa kamu guda. Ya yi ɗamara da shi wajen cinyarsa ta dama a ƙarƙashin tufafinsa.