Littafi Mai Tsarki

L. Mah 20:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Dukan jama'ar Isra'ila fa suka fito tun daga Dan a arewa har zuwa Biyer-sheba a kudu da kuma Gileyad daga gabas. Suka hallara gaba ɗaya a gaban Ubangiji a Mizfa.

2. Dukan shugabannin kabilar Isra'ila suna cikin wannan taron jama'ar Allah. Sojojin ƙafa yawansu ya kai dubu ɗari huɗu (400,000).

3. Mutanen Biliyaminu kuwa sun ji labari sauran Isra'ilawa sun haura zuwa Mizfa. Isra'ilawa suka tambayi Balawen suka ce, “Ka faɗa mana yadda wannan mugun abu ya auku.”

4. Balawe, mai ƙwarƙwarar da ka kashe, ya amsa ya ce, “Ni da ƙwarƙwarata muna biyo Gibeya ta Biliyaminu mu kwana.

5. Sai mutanen Gibeya suka kewaye gidan da nake da dare, suna neman kashe ni, da ba su same ni ba, sai suka yi wa ƙwarƙwarata faɗe har ya kai ta ga mutuwa.

6. Ni kuwa na ɗauki gawarta na yanyanka gunduwa gunduwa na aika cikin ƙasar gādon Isra'ila duka, gama waɗannan mutane sun aikata abin ƙyama da abin kunya ga dukan Isra'ila.