Littafi Mai Tsarki

L. Mah 20:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Dukan jama'ar Isra'ila fa suka fito tun daga Dan a arewa har zuwa Biyer-sheba a kudu da kuma Gileyad daga gabas. Suka hallara gaba ɗaya a gaban Ubangiji a Mizfa.

2. Dukan shugabannin kabilar Isra'ila suna cikin wannan taron jama'ar Allah. Sojojin ƙafa yawansu ya kai dubu ɗari huɗu (400,000).