Littafi Mai Tsarki

L. Mah 2:8-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Bawan Ubangiji, Joshuwa ɗan Nun, ya rasu yana da shekara ɗari da goma.

9. Suka binne shi a Timnat-sera a ƙasar tuddai ta Ifraimu, arewa da dutsen Ga'ash, a ƙasar gādonsa.

10. Dukan tsarar Joshuwa sun rasu, waɗanda suke tasowa kuwa suka manta da Ubangiji da abubuwan da ya yi wa Isra'ila.

11. Jama'ar Isra'ila kuwa suka yi wa Ubangiji zunubi, wato suka bauta wa gunkin nan mai suna Ba'al.

12. Suka bar yi wa Ubangiji Allah na kakanninsu sujada, wanda ya fisshe su daga ƙasar Masar. Suka fara yi wa allolin mutanen da suke zaune kewaye da su sujada. Suka rusuna wa allolin, da haka suka sa Ubangiji ya yi fushi.

13. Suka bar yi wa Ubangiji sujada suka bauta wa gumakan nan, wato Ba'al da Ashtarot.

14. Ubangiji kuwa ya husata da Isra'ilawa, ya bashe su ga waɗanda za su washe su. Ya sa magabtansu da suke kewaye da su suka sha ƙarfinsu, har ya zama Isra'ilawa ba su iya kāre kansu daga maƙiyansu ba.

15. A duk sa'ad da suka tafi yaƙi sai Ubangiji ya yi gāba da su kamar dai yadda ya faɗa. Saboda haka suka shiga wahala ƙwarai.

16. Sa'an nan Ubangiji ya naɗa musu mahukunta masu ƙarfi da suka cece su daga waɗanda suka washe su.