Littafi Mai Tsarki

L. Mah 19:26-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. Da gari ya waye, ƙwarƙwarar ta zo ta fāɗi a ƙofar gidan tsohon, inda maigidanta ya sauka, tana nan har hantsi ya cira.

27. Sa'ad da Balawen ya tashi da safe, ya buɗe ƙofa, ya fita domin ya kama hanyarsa, sai ga ƙwarƙwararsa kwance a ƙofar gida, da hannuwanta a dokin ƙofar.

28. Ya ce mata, “Tashi mu tafi.” Amma ba amsa. Sai ya aza gawarta a kan jaki, sa'an nan ya kama hanya zuwa gida.

29. Da ya isa gida, ya ɗauki wuƙa ya yanyanka gawar ƙwarƙwararsa gunduwa gunduwa har goma sha biyu, ya aika a ko'ina cikin dukan ƙasar Isra'ila.

30. Dukan wanda ya ga haka sai ya ce, “Ba mu taɓa ganin irin wannan abu ba, ba a kuwa taɓa yin haka ba tun daga ranar da Isra'ilawa suka fito daga ƙasar Masar sai yau. Ku yi tunani, me za mu yi a kan wannan al'amari?”