Littafi Mai Tsarki

L. Mah 18:7-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Saboda haka mutanen nan biyar suka tashi, suka zo Layish, suka ga mutane suna zamansu a huce, kamar Sidoniyawa. Ba su da rigima, natsattsu ne, ba su jayayya da kowa, suna da wadata. Suna nesa da Sidoniyawa, ba su sha'anin kome da kowa.

8. Da mutanen nan biyar suka koma wurin 'yan'uwansu a Zora da Eshtawol, sai 'yan'uwan suka tambaye su labarin tafiyarsu.

9. Suka ce, “Ku tashi, mu tafi mu fāɗa musu, gama mun ga ƙasar tana da ni'ima ƙwarai. Kada ku zauna ku ɓata lokaci, ku shiga ku mallake ta!

10. Idan kuka je za ku tarar da mutane suna zama a sake. Ƙasar kuwa babba ce, tana da dukan abin da ɗan adam yake bukata.”

11. Mutum ɗari shida daga kabilar Dan suka yi shirin yaƙi, suka kama hanya daga Zora da Eshtawol.

12. Suka tafi suka kafa sansani a yammacin Kiriyat-yeyarim, birni ne a Yahudiya. Saboda haka ake kiran wurin Mahanedan, wato sansanin Dan, har wa yau.

13. Daga can suka wuce zuwa ƙasar tudu ta Ifraimu, suka zo gidan Mika.

14. Mutum biyar ɗin nan da suka tafi leƙen asirin ƙasar Layish, suka ce wa abokan tafiyarsu, “Ko kun san akwai gunkin itace cikin gidajen nan? Akwai kuma gunki na zubi, da kan gida, da falmaran dominsu. Me ya kamata mu yi musu?”

15. Sai suka juya zuwa gidan Mika, inda saurayin nan Balawe yake, suka gaishe shi.

16. Danawa ɗari shida ɗin da suka yi shirin yaƙi, suka tsaya a bakin ƙofa.

17. Amma mutum biyar ɗin nan da suka tafi leƙen asirin ƙasar suka shiga kai tsaye, suka ɗauki gunkin da aka yi da itace, da falmaran, da kan gida, da gunki na zubi. Firist ɗin kuwa ya tsaya a bakin ƙofa tare da mutum ɗari shida ɗin nan masu shirin yaƙi.

18. Sa'ad da mutum biyar ɗin nan suka shiga gidan Mika suka ɗauki falmaran, da sassaƙaƙƙen gunki, da kan gida, da gunki na zubi, sai firist ɗin ya ce musu, “Me kuke yi?”