Littafi Mai Tsarki

L. Mah 17:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Akwai wani mutum a ƙasar tudu ta Ifraimu, da ake kira Mika.

2. Shi ne ya ce wa mahaifiyarsa, “Sa'ad da aka sace miki tsabar azurfan nan dubu da ɗari ɗaya (1,100), kin hurta la'ana a kan ɓarayin, na kuwa ji ki. To, ga shi, azurfar na wurina, ni na ɗauka.”Sai mahaifiyarsa ta ce, “Allah ya sa maka albarka, ɗana.”

3. Ya mayar wa mahaifiyarsa da azurfar dubu da ɗari (1,100). Mahaifiyarsa ta ce, “Domin kada la'anar ta kama ɗana, ina ba da wannan azurfa ga Ubangiji da zuciya ɗaya. Ana iya sassaƙa gunki a kuma yi na zubi saboda haka zan ba ka ita.”

4. Da ya mayar mata da azurfar, ta ɗibi azurfa ɗari biyu ta ba maƙerin azurfa, shi kuwa ya sassaƙa gunki ya kuma yi na zubi. Aka ajiye su a gidan Mika.