Littafi Mai Tsarki

L. Mah 15:7-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Samson ya ce musu, “Wato haka kuka yi! To, na rantse, ba zan bari ba sai na rama!”

8. Ya kuwa fāɗa musu, ya kashe su da yawa. Sa'an nan ya tafi ya zauna a kogon dutsen Itam.

9. Filistiyawa suka haura, suka kafa sansani a Yahudiya, suka bazu a cikin Lihai.

10. Mutanen Yahuza suka ce, “Me ya sa kuka kawo mana yaƙi?”Filistiyawa suka ce, “Mun zo ne domin mu kama Samson, mu yi masa kamar yadda ya yi mana.”

11. Sa'an nan mutum dubu uku na Yahuza suka gangara zuwa kogon dutsen Itam. Suka ce wa Samson, “Ba ka sani ba Filistiyawa ne suke mulkinmu? Me ya sa ka yi mana haka?”Shi kuwa ya amsa musu, ya ce, “Kamar yadda suka yi mini, haka ni kuma na yi musu.”

12. Suka ce masa, “Mun gangara zuwa wurinka don mu ɗaure ka, mu miƙa ka gare su.”Samson ya ce musu, “Ku rantse mini idan ba ku ne da kanku kuke so ku kashe ni ba.”

13. Suka ce masa, “A'a, ba za mu kashe ka ba, mu dai za mu kama ka, mu miƙa ga Filistiyawa.” Sa'an nan suka ɗaure shi da sababbin igiyoyi biyu, suka sauko da shi daga dutsen.

14. Sa'ad da ya zo Lihai, sai Filistiyawa suka sheƙo a guje suna ihu suka nufo shi. Ruhun Ubangiji ya sauko kansa da iko, sai igiyoyin da suke a ɗaure da shi suka tsintsinke kamar zaren da ya kama wuta.

15. Ya kuwa sami sabon muƙamuƙin jaki, ya ɗauka ya kashe mutum dubu da muƙamuƙin.

16. Sa'an nan Samson ya raira waƙa ya ce.“Da muƙamuƙin jaki na kashe mutum dubu,Da muƙamuƙin jaki na tsiba su tsibi-tsibi.”