Littafi Mai Tsarki

L. Fir 2:11-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. A kowace hadaya ta gari da za a kawo wa Ubangiji, ba za a sa yisti ba, gama ba za a yi hadayar ƙonawa ga Ubangiji da yisti, ko da zuma ba.

12. Amma a iya kawo su kamar hadayar nunan fari ga Ubangiji, sai dai ba za a ƙona su a kan bagade ba, kamar hadaya ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi.

13. Sai a sa gishiri a kowace hadaya ta gari, kada a rasa sa gishirin alkawarin Allah a hadaya ta gari. A sa gishiri a dukan hadayu.

14. Idan za a yi hadaya ta gari daga cikin nunan fari ga Ubangiji, sai a miƙa hadaya ta nunan fari da ɗanyen hatsi wanda aka gasa aka ɓarza.

15. Za a zuba masa mai, a barbaɗa masa lubban, gama hadaya ce ta gari.

16. Firist kuwa zai ƙone wani kashi daga cikin ɓarzajjen hatsin a gauraye da man, da dukan lubban don tunawa, gama hadaya ce ta ƙonawa ga Ubangiji.