Littafi Mai Tsarki

L. Fir 13:46-54 Littafi Mai Tsarki (HAU)

46. Muddin yana da cutar, zai zama marar tsarki. Zai zauna shi kaɗai a bayan zango.

47. Idan ana tsammani akwai cutar kuturta a rigar ulu ko ta lilin,

48. ko a tariyar zaren, ko a waɗari, ko a lilin, ko a ulu, ko a cikin fata, ko cikin kowane abu da aka yi da fata,

49. idan cutar ta zama kore-kore, ko jaja-jaja a rigar, ko a fatar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a kan abin da aka yi da fata, wannan cuta kuturta ce, sai a nuna wa firist.

50. Firist zai dudduba cutar, ya ajiye abin da yake da cutar har kwana bakwai.

51. A rana ta bakwai ɗin zai sāke dudduba cutar, idan cutar ta yaɗu a rigar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a fatar, komene ne za a yi da fata, wannan cuta muguwar kuturta ce, abin zai zama marar tsarki.

52. Zai ƙone rigar, ko tariyar zaren, ko waɗari na ulu ko na lilin, ko abin da dai aka yi da fata wanda yake da cutar, gama muguwar kuturta ce.

53. Amma idan firist ya dudduba ya ga cutar ba ta yaɗu a rigar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a abin da aka yi da fata ba,

54. sai firist ya umarta a wanke abin da yake da cutar, ya sāke ajiye shi har kwana bakwai kuma.