Littafi Mai Tsarki

L. Fir 1:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya kirawo Musa, ya yi masa magana daga cikin alfarwa ta sujada, ya ce

2. ya ba Isra'ilawa ka'idodin nan.Sa'ad da kowane mutum a cikinsu zai kawo sadaka ga Ubangiji, sai ya kawo sadakarsa daga cikin garkunansa na shanu, da na tumaki, da na awaki.

3. Idan sadakarsa ta hadayar ƙonawa ce daga cikin garken shanu, sai ya ba da namiji marar lahani, zai miƙa shi a ƙofar alfarwa ta sujada domin sadakar ta zama abar karɓa a gaban Ubangiji.

4. Sai ya ɗibiya hannunsa a kan kan hadaya ta ƙonawar, za a karɓa masa, a kuwa yi masa gafara.

5. Sa'an nan zai yanka ɗan bijimin a gaban Ubangiji. 'Ya'yan Haruna maza, firistoci, za su miƙa jinin a bagaden da yake a ƙofar alfarwa ta sujada za su kuma yayyafa jinin a kewaye da shi.

6. Sai mai hadayar ya feɗe dabbar, ya yanyanka ta gunduwa-gunduwa.

7. Sa'an nan 'ya'yan Haruna maza, firistoci, za su hura wuta a bisa bagaden, su jera itace daidai a wutar.