Littafi Mai Tsarki

K. Mag 1:12-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Ba mu damu da ransu da lafiyarsu ba, mu dai mu tafi mu kashe su, mu hallaka su ɗungum.

13. Za mu sami dukiya iri iri, mu cika gidajenmu da ganima!

14. Ka zo ka haɗa kai da mu, dukanmu kuwa za mu raba abin da muka sato.”

15. Ɗana, kada ka gama kanka da irin waɗannan mutane, ka yi nesa da su.

16. Ba su kasalar aikata mugunta, kullum a shirye suke su yi kisankai.

17. Ba shi da amfani a kafa tarko a idon tsuntsun da ake so a kama.

18. Amma waɗannan irin mutane kansu suke kafa wa tarko. Ba za su kama kome ba, sai rayukansu.

19. Yin fashi yakan zama sanadin mutuwar ɗan fashi a koyaushe. Wannan shi ne abin da yakan sami kowane mutum da ya kama sana'ar sata.

20. Ku kasa kunne! Hikima tana kira a tituna da a kasuwoyi.

21. Tana kira da ƙarfi a ƙofofin birni, a duk inda mutane suke tattaruwa.

22. Ta ce, “Wawayen mutane! Har yaushe za ku yi ta kasancewa haka? Har yaushe za ku daina jin daɗin yi wa mai ilimi ba'a? Faufau ba za ku taɓa koya ba?

23. Ku kasa kunne lokacin da nake tsauta muku, zan ba ku shawara mai kyau, mu yi tarayya cikin ilimina.

24. Ina ta kiranku ina gayyatarku ku zo, amma ba ku kula ba, ba ku mai da hankali gare ni ba.

25. Kun ƙi bin shawarwarina duka, ba ku yarda in gyara kuskurenku ba.