Littafi Mai Tsarki

Fit 39:3-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. An kuma buga zinariya fake-fake, suka yanyanka ta zare-zare don su yi saƙa da ita tare da zane na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, da na lallausan lilin, aikin gwani mai fasaha.

4. Suka yi wa falmaran kafaɗu, sa'an nan suka haɗa su a gefenta biyu na sama.

5. Gwanin masaƙi ya saƙa abin ɗamarar falmaran. Da irin kayan da aka saƙa falmaran ne aka saƙa abin ɗamarar, wato da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da zaren lallausan lilin kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

6. Sai aka gyaggyarta duwatsu masu daraja aka jera su cikin tsaiko na zinariya. Aka zana sunayen 'ya'yan Isra'ila a kan duwatsun kamar yadda akan yi hatimi.

7. Aka sa su a kan kafaɗun falmaran don su zama duwatsun tunawa da Isra'ila kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

8. Aka kuma yi ƙyallen maƙalawa a ƙirji da gwaninta kamar yadda aka yi wa falmaran aiki da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin.

9. Ƙyallen maƙalawa a ƙirji murabba'i ne, aka ninka shi biyu, tsawonsa da fāɗinsa kamu ɗaya ɗaya ne.

10. Sai suka sa jeri huɗu na duwatsu masu daraja a bisansa. A jeri na fari aka sa yakutu, da tofaz, da zumurrudu.