Littafi Mai Tsarki

Fit 39:16-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Suka yi tsaiko biyu na zinariya da ƙawane biyu na zinariya. Sai suka sa ƙawanen nan biyu a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji.

17. Suka kuma zura sarƙoƙin nan biyu na zinariya a ƙawanen nan biyu na zinariya na gyaffan ƙyallen maƙalawa a ƙirji.

18. Sai suka maƙala waɗancan bakin sarƙoƙin zinariya a tsaikon nan biyu, sa'an nan suka rataya su a kafaɗun falmaran daga gaba.

19. Suka kuma yi ƙawane biyu na zinariya, suka sa su a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji daga ciki kusa da falmaran.

20. Suka yi waɗansu ƙawane biyu na zinariya, suka maƙala su daga ƙasa a gaban kafaɗu biyu na falmaran kusa da mahaɗin a bisa abin ɗamarar falmaran.

21. Sai suka ɗaure ƙawanen ƙyallen maƙalawa a ƙirjin a ƙawanen falmaran da shuɗiyar igiya don ƙyallen maƙalawa a ƙirji ya kwanta lif a bisa kan abin ɗamarar falmaran don kada ya kwance daga falmaran, sun yi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

22. Ya kuma saƙa taguwa ta falmaran da shuɗi duka.

23. An yi wa taguwar wuyan wundi kamar sulke, aka daje wuyan don kada ya kece.

24. A karbun taguwar, suka yi fasalin 'ya'yan rumman da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin.

25. Suka kuma yi ƙararrawa da zinariya tsantsa, suka sa su a tsakankanin fasalin 'ya'yan rumman kewaye da karbun taguwa.

26. An jera su bi da bi, wato fasalin rumman yana biye da ƙararrawa. Haka aka jera su kewaye da karbun taguwar yin aiki, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

27. Suka saƙa zilaika da lallausan zaren lilin don Haruna da 'ya'yansa.

28. Suka kuma yi rawani, da huluna, da mukurai da lallausan lilin.