10. Sai suka sa jeri huɗu na duwatsu masu daraja a bisansa. A jeri na fari aka sa yakutu, da tofaz, da zumurrudu.
11. A jeri na biyu aka sa turkos, da saffir, da daimon.
12. A jeri na uku aka sa yakinta, da idon mage, da ametis.
13. A jeri na huɗu aka sa beril, da onis, da yasfa. Aka sa su cikin tsaiko na zinariya.
14. An zana sunayen 'ya'yan Isra'ila goma sha biyu a kan duwatsu masu daraja kamar yadda akan yi hatimi.
15. Sai suka yi tukakkun sarƙoƙi na zinariya tsantsa a kan ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
16. Suka yi tsaiko biyu na zinariya da ƙawane biyu na zinariya. Sai suka sa ƙawanen nan biyu a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
17. Suka kuma zura sarƙoƙin nan biyu na zinariya a ƙawanen nan biyu na zinariya na gyaffan ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
18. Sai suka maƙala waɗancan bakin sarƙoƙin zinariya a tsaikon nan biyu, sa'an nan suka rataya su a kafaɗun falmaran daga gaba.
19. Suka kuma yi ƙawane biyu na zinariya, suka sa su a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji daga ciki kusa da falmaran.
20. Suka yi waɗansu ƙawane biyu na zinariya, suka maƙala su daga ƙasa a gaban kafaɗu biyu na falmaran kusa da mahaɗin a bisa abin ɗamarar falmaran.
21. Sai suka ɗaure ƙawanen ƙyallen maƙalawa a ƙirjin a ƙawanen falmaran da shuɗiyar igiya don ƙyallen maƙalawa a ƙirji ya kwanta lif a bisa kan abin ɗamarar falmaran don kada ya kwance daga falmaran, sun yi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.