Littafi Mai Tsarki

Fit 30:19-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. A wurin ne Haruna da 'ya'yansa maza za su wanke hannuwansu da ƙafafunsu.

20. Sa'ad da suke shiga cikin alfarwa ta sujada ko sa'ad da suke kusatar bagade don su miƙa hadaya ta ƙonawa da wuta ga Ubangiji, sai su yi wanka don kada a kashe su.

21. Su wanke hannuwansu da ƙafafunsu don kada su mutu. Yin wannan zai zama musu da zuriyarsu farilla dukan zamanansu.”

22. Ubangiji kuma ya ce wa Musa,

23. “Ɗauki kayan yaji masu kyan gaske, ruwan mur na shekel ɗari biyar, da kirfa mai daɗin ƙanshi na shekel ɗari biyu da hamsin, da turaren wuta mai ƙanshi na shekel ɗari biyu da hamsin,

24. da kashiya na shekel ɗari biyar bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi, da moɗa ɗaya na man zaitun.

25. Da waɗannan za ku yi man keɓewa mai tsarki yadda mai yin turare yake yi, zai zama man keɓewa mai tsarki.

26. Za a shafa wa alfarwa ta sujada da akwatin alkawari wannan mai.

27. A kuma shafa wa teburin da kayayyakinsa, da alkukin da kayayyakinsa, da bagaden ƙona turare,

28. da bagaden hadaya ta ƙonawa da kayayyakinsa, da daron da gammonsa.

29. Ta haka za a tsarkake su domin su zama masu tsarki sosai. Duk abin da ya taɓa su zai tsarkaka.

30. Za ka zuba wa Haruna da ya'yansa maza mai, ka keɓe su domin su zama firistocina masu yi mini aiki.

31. Sai ka faɗa wa Isra'ilawa cewa, ‘Wannan mai, mai tsarki ne a gare ni domin keɓewa a dukan zamananku.