Littafi Mai Tsarki

Fit 25:23-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. “Ku yi tebur da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi.

24. Ku dalaye shi da zinariya tsantsa, ku kuma yi masa ado kewaye da gurun zinariya.

25. Za ku yi wa tebur ɗin dajiya mai fāɗin tafin hannu, ku kuma yi wa dajiyar ado da gurun zinariya.

26. Za ku yi ƙawanya huɗu da zinariya, ku sa a kusurwa huɗu na ƙafafun teburin.

27. Ƙawanen za su kasance kusa da dajiyar don su riƙe sandunan ɗaukar teburin.

28. Ku yi sanduna da itacen ƙirya, sa'an nan ku dalaye su da zinariya. Da su za a riƙa ɗaukar teburin.

29. Da zinariya tsantsa kuma za ku yi farantansa, da kwanonin tuya, da butocinsa, da kwanoninsa domin yin hadayu na sha.

30. Kullum za ku riƙa ajiye gurasar da kuke kawo mini a bisa teburin.”

31. “Ku kuma yi alkuki da zinariya tsantsa. Ku yi gindinsa da gorar jikinsa da ƙerarriyar zinariya. Ƙoƙuna, da mahaɗai, da furanninsa a haɗe da shi za ku yi su.

32. Alkukin ya kasance da rassa shida, rassa uku a kowane gefe.

33. A kowane reshe na alkuki za a yi ƙoƙuna uku masu kamar tohon almond. Ya kasance kuma da mahaɗai da furanni.

34. Za a yi wa gorar alkukin ƙoƙuna huɗu masu kamar tohon almond, da mahaɗai da furanni.

35. A gindin kowane reshe biyu za a yi mahaɗi ɗaya.

36. Da mahaɗai da rassan za su kasance a haɗe da alkukin. Da ƙerarriyar zinariya za a yi su.