Littafi Mai Tsarki

Fit 2:21-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Musa kuwa ya yarda ya zauna tare da Reyuwel. Sai ya aurar wa Musa da 'yarsa Ziffora.

22. Ita kuwa ta haifa masa ɗa, ya raɗa masa suna Gershom, gama ya ce, “Baƙo ne ni, a baƙuwar ƙasa.”

23. Ana nan, a kwana a tashi, sai Sarkin Masar ya rasu. Jama'ar Isra'ila suka yi nishi, suka yi kuka kuma saboda bautarsu, kukansu na neman gudunmawa ya kai gun Allah.

24. Allah kuwa ya ji nishinsu, sai ya tuna da alkawarinsa da ya yi wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.

25. Allah ya dubi jama'ar Isra'ila, ya kuwa kula da su.