Littafi Mai Tsarki

Fit 18:21-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Ka kuma zaɓa daga cikin jama'a isassun mutane, masu tsoron Allah, amintattu, waɗanda suke ƙyamar cin hanci. Ka naɗa su shugabannin jama'a na dubu dubu da na ɗari ɗari, da na hamsin hamsin, da na goma goma.

22. Za su yi wa mutane shari'a koyaushe, amma kowace babbar matsala sai su kawo maka, ƙaramar matsala kuwa su yanke da kansu. Da haka za su ɗauki nauyin jama'a tare da kai don ya yi maka sauƙi.

23. In ka bi wannan shawara, in kuma Allah ya umarce ka da yin haka, za ka iya ɗaukar nawayar jama'ar. Mutane duka kuwa za su yi zamansu lafiya.”

24. Musa kuwa ya saurari maganar surukinsa, ya yi abin da ya ce duka.

25. Sai Musa ya zaɓi isassun mutane daga cikin Isra'ilawa ya naɗa su shugabannin jama'a na dubu dubu, da na ɗari ɗari, da na hamsin hamsin, da na goma goma.

26. Suka yi ta yi wa jama'a duka shari'a kullayaumin, amma matsaloli masu wuya sukan kawo wa Musa, ƙananan kuwa sukan yanke da kansu.

27. Sa'an nan Musa ya sallami surukinsa, ya koma garinsu.