Littafi Mai Tsarki

Esta 5:5-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Sarki kuwa ya ce, “A zo da Haman maza, mu yi abin da Esta take so.” Sai sarki da Haman suka tafi liyafar da Esta ta shirya.

6. Sa'ad da suke shan ruwan inabi, sai sarki ya tambayi Esta, “Mece ce bukatarki? Za a biya miki ko da rabin mulkina ne.”

7. Sai Esta ta ce, “Bukatata, da roƙona ke nan,

8. idan na sami tagomashi a wurin sarki, idan kuma sarki ya yarda ya biya bukatata da roƙona, to, bari sarki da Haman su zo liyafar da zan yi musu, gobe kuwa zan yi abin da sarki ya faɗa.”

9. Ran nan Haman ya fita da murna da farin ciki, amma da ya ga Mordekai a ƙofar sarki, Mordekai kuwa bai tashi ba, bai kuma yi rawar jiki a gabansa ba, sai ya husata ƙwarai.