Littafi Mai Tsarki

Ayu 1:9-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Shaiɗan ya amsa, ya ce, “A banza Ayuba yake yi maka sujada?

10. Ai, don ka kiyaye shi ne, shi da iyalinsa, da dukan abin da yake da shi. Ka kuma sa wa duk abin da yake yi albarka, ka kuwa ba shi shanun da suka isa su cika dukan ƙasan nan.

11. Amma da a ce za ka raba shi da dukan abin hannunsa, to, da zai fito fili yă zage ka ƙiri ƙiri.”

12. Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “To, shi ke nan, dukan abin hannunsa yana cikin ikonka, amma shi kansa kada ka cuce shi.” Sai Shaiɗan ya tafi.

13. Wata rana 'ya'yan Ayuba suna shagali a gidan wansu,

14. sai ga jakada ya zo wurin Ayuba a guje, ya ce, “Muna huɗar gona da shanu, jakuna suna kiwo a makiyayar da suke kusa da wurin,

15. sai Sabiyawa suka auka musu farat ɗaya, suka sace su duka, suka kuma karkashe duk barorinka, sai ni kaɗai na tsira, na zo in faɗa maka.”