Littafi Mai Tsarki

Ayu 1:12-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “To, shi ke nan, dukan abin hannunsa yana cikin ikonka, amma shi kansa kada ka cuce shi.” Sai Shaiɗan ya tafi.

13. Wata rana 'ya'yan Ayuba suna shagali a gidan wansu,

14. sai ga jakada ya zo wurin Ayuba a guje, ya ce, “Muna huɗar gona da shanu, jakuna suna kiwo a makiyayar da suke kusa da wurin,

15. sai Sabiyawa suka auka musu farat ɗaya, suka sace su duka, suka kuma karkashe duk barorinka, sai ni kaɗai na tsira, na zo in faɗa maka.”

16. Kafin yă gama magana, sai wani bara ya zo, ya ce, “Tsawa ta kashe tumaki da makiyayansu duka, ni kaɗai na tsira, na zo in faɗa maka.”

17. Kafin yă gama magana, sai wani bara ya zo, ya ce, “Ƙungiyoyin mahara uku na Kaldiyawa suka auka mana, suka kwashe raƙuma duka, suka kuma karkashe barorinka duka, sai ni kaɗai na tsira, na zo in faɗa maka.”

18. Kafin yă gama magana, sai wani bara ya zo, ya ce, “Sa'ad da 'ya'yanka suke liyafa a gidan wansu,

19. sai hadiri ya taso daga hamada, ya rushe gidan, ya kashe 'ya'yanka duka, ni kaɗai na tsira na zo in faɗa maka.”

20. Sai Ayuba ya tashi, ya kyakkece tufafinsa don baƙin ciki. Ya aske kansa, ya fāɗi ƙasa,

21. ya ce, “Ban shigo duniya da kome ba, ba kuma zan fita cikinta da kome ba. Ubangiji ya bayar, shi ne kuma ya karɓe, yabo ya tabbata ga sunansa.”

22. Ko da yake waɗannan al'amura duka sun faru, duk da haka Ayuba bai sa wa Allah laifi ba.