Littafi Mai Tsarki

A.m. 7:8-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Ya kuma yi masa alkawari game da kaciya. Ta haka, da Ibrahim ya haifi Ishaku, ya yi masa kaciya a rana ta takwas. Ishaku ya haifi Yakubu, Yakubu kuma ya haifi kakanninmu sha biyun nan.

9. “Kakannin nan kuwa, da yake suna kishin Yusufu, suka sayar da shi, aka kai shi Masar. Amma Allah na tare da shi,

10. ya kuma tsamo shi daga dukan wahala tasa, ya ba shi farin jini da hikima a gun Fir'auna, Sarkin Masar, shi kuwa ya naɗa shi mai mulkin Masar, ya kuma danƙa masa jama'ar gidansa duka.

11. To, sai wata yunwa ta auku a dukan ƙasar Masar da ta Kan'ana, game da matsananciyar wahala, har kakanninmu suka rasa abinci.

12. Amma da Yakubu ya ji akwai alkama a Masar, ya aiki kakanninmu tafiyar farko.

13. A tafiyarsu ta biyu Yusufu ya sanar da kansa ga 'yan'uwansa, asalinsa kuma ya sanu ga Fir'auna.

14. Sai Yusufu ya aika wa ubansa Yakubu yă zo, da kuma dukan 'yan'uwansa, mutum saba'in da biyar.

15. Sai Yakubu ya tafi Masar. A can ma ya mutu, shi da kakanninmu.

16. Sai aka ɗebo su aka mai da su Shekem, aka sa su a kabarin da Ibrahim ya saya da kuɗi azurfa a wurin 'ya'yan Hamor a nan Shekem.

17. “Amma da lokacin cikar alkawarin da Allah ya yi wa Ibrahim ya gabato, jama'ar suka ƙaru, suka yawaita ƙwarai a ƙasar Masar,

18. har aka yi wani sarki a Masar, wanda bai san ko wane ne Yusufu ba.