Littafi Mai Tsarki

A.m. 28:4-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Da mutanen garin suka ga mugun ƙwaron nan a makale a hannun Bulus, suka ce wa juna, “Lalle mutumin nan mai kisankai ne, kun ga ko da yake ya tsira daga bahar, duk da haka alhaki yana binsa sai ya mutu.”

5. Bulus kuwa ya karkaɗe ƙwaron a cikin wutar, bai kuwa ji wani ciwo ba.

6. Su kuwa suna zaton wurin zai kumbura, ko kuwa farat ɗaya ya fāɗi matacce. Amma da aka daɗe suka ga ba abin da ya same shi, suka sāke magana suka ce lalle shi wani Allah ne.

7. A nan kusa kuwa akwai wani fili, mallakar shugaban tsibirin nan, mai suna Babiliyas. Shi ne ya karɓe mu, ya sauke mu a cikin martaba har kwana uku.

8. Ashe, uban Babiliyas yana a kwance, yana fama da zazzaɓi da atuni. Sai Bulus ya shiga wurinsa ya yi addu'a, ya ɗora masa hannu ya warkar da shi.

9. Da aka yi haka sai duk sauran marasa lafiya a tsibirin suka riƙa zuwa ana warkar da su.

10. Suka yi mana kyauta mai yawa, da za mu tashi a jirgin ruwa kuma, suka yi ta tara mana duk irin abubuwan da muke bukata.