Littafi Mai Tsarki

A.m. 23:8-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Sadukiyawa sun ce, wai ba tashin matattu, ba kuma mala'iku, ko ruhu. Farisiyawa kuwa sun tsaya a kan cewa duk akwai.

9. Sai ƙasaitacciyar hargowa ta tashi, waɗansu malamai kuma na ɗariƙar Farisiyawa suka miƙe a tsaye, suka yi ta yin matsananciyar jayayya, suna cewa, “Mu ba mu ga laifin mutumin nan ba. In wani ruhu ne ko mala'ika ya yi masa magana fa?”

10. Da gardamar ta yi tsanani, don gudun kada su yi kaca-kaca da Bulus, shugaban ya umarci sojan su sauka su ƙwato shi daga wurinsu ƙarfi da yaji, su kawo shi a kagarar soja.

11. Da daddare sai Ubangiji ya tsaya a kusa da Bulus, ya ce, “Ka yi ƙarfin hali, don kamar yadda ka shaide ni a Urushalima, haka kuma lalle ne ka shaide ni a Roma.”

12. Da gari ya waye, Yahudawa suka gama baki suka yi rantsuwa, cewa ba za su ci ba, ba za su sha ba, sai sun kashe Bulus.

13. Waɗanda suka ƙulla wannan makirci kuwa sun fi mutum arba'in.

14. Sai suka je wurin manyan firistoci da shugabanni, suka ce, “Mun yi wata babbar rantsuwa, cewa za mu zauna ba ci ba sha sai mun kashe Bulus.

15. Saboda haka, yanzu ku da majalisa ku shaida wa shugaban soja ya kawo muku shi, kamar kuna so ne ku ƙara bincika maganarsa sosai, mu kuwa a shirye muke mu kashe shi kafin ya iso.”

16. To, ɗan 'yar'uwar Bulus ya ji labarin farkon da za su yi, ya kuma je ya shiga kagarar soja ya gaya wa Bulus.

17. Bulus kuwa ya kira wani jarumi ya ce, “Ka kai saurayin nan wurin shugaba, yana da wata magana da zai faɗa masa.”

18. Sai jarumin ya ɗauki saurayin ya kai shi gun shugaba, ya ce, “Ɗan sarƙan nan, Bulus, ya kira ni, ya roƙe ni in kawo saurayin nan a wurinka, don yana da wata maganar da zai gaya maka.”

19. Sai shugaban ya kama hannun saurayin, ya ja shi a waje ɗaya, ya tambaye shi a keɓance, “Wace magana za ka gaya mini?”

20. Yaron ya ce, “Yahudawa sun ƙulla za su roƙe ka ka kai musu Bulus majalisa gobe, kamar suna so su ƙara bincika maganarsa sosai.